(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kwamitin likitocin kasar Sudan ya fitar da bayani da ke cewa,a yau Litinin mutane 5 ne suka rasa rayukansu a garin Abyad babban birnin Jihar Kurdufan, a lokacin da suke gudanar da wani jerin gwano.
Bayanin ya ce, 4 daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu dalibai ne, da kuma wani farar hula mutumin gari guda, kuma wasu masu harbi daga nesa suka harbe su, kuma suka same su kai tsaye, yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka.
A ranar 17 ga wanann wata na Yuli ne dai bangarorin soji da kuma na jam'iyyun adawa da farar hula suka cimma matsaya kan kafa gwamnatin rikon kwarya, wadda za ta jagoranci lamurran kasar tsawon watanni 39.
/129
30 Yuli 2019 - 06:29
Lambar labari: 965754
Akalla mutane 5 ne suka rasa rayukansu daga cikin masu gudanar da wani jerin gwano a yau a Litinin a birnin Abyad da ke jihar Kurdufan a tsakiya Sudan.